English large_stringlengths 3 611 | Target Language large_stringlengths 3 437 |
|---|---|
They have storage facilities where they protect their produce until they are sold. | Suna da guraren ajiya inda suke kare amfanin gona daga lalacewa har su siyar. |
A. The important of agriculture to the farmer. | A. Amfanin noma ga manoma. |
Depressed part of the land is easily waterlogged. | Yankin fili mai rami-rami yana da sauƙin tara ruwa. |
A. Routine vaccination of wild animal B. conservation of forest resources C. specification of size of tree to be felled D. grading of timbers for export | A. Alurar riga kafi na namun daji B. Kiyaye albarkatun gandun daji C. Takamaiman girman bishiyar da za a sare D. grading na katako don fitarwa zuwa waje |
-It involves the use of complicated and expensive equipment. | -Ya ƙunshi amfani da kayan aiki masu sarkakiya da tsada. |
Banks may not provide loans and produce may not sell at the right price to make more money to reinvest in the business. | Bankuna za su iya ƙin ba da lamuni, kuma ana iya kasa sayar da amfanin gona a farashin da ya dace don samun kuɗin za a ƙara zubawa a harkar. |
4. They are ease to handle compared to organic manures. | 4. Suna da sauƙin amfani idan ka haɗa su dana gargajiya. |
As raw materials (e.g. limestone, dolomite, marble) for our industries Sources of minerals (food) rock salt such as sodium chloride (table salt). | A matsayin albarkatun ƙasa (misali farar ƙasa, nau'in farar ƙasa na dolomait , marmara) a matsayin hanyoyin samun ma'adinai (abinci) dutsen gishiri, kamar sodiyum koloraid (gishiri) ga masana'antunmu. |
c. Explain two disadvantages of branding 2mks | c. Bayyana rashin alfanun alamta kaya(branding) biyu Maki 2 |
CEREAL CROPS:These crops belong to the grass family called Gramineae. | HATSI: Waɗannan tsirran na ƙarƙashin iyalan ciyawa ne da ake kira Gramineae. |
A. River Basin Development Authority B. Operation Feed the Nation C.Expanded Programme on Immunization Programme D. Green Revolution | A. Hukumar Raya Albarkatun Ruwa B. Shirin Ciyar da Ƙasa C. Faɗaɗa Shirin Kan Shirin Rigakafi
D. Koren Shirin Sauyin Noma |
These three programmes were introduced by the former military presidents-Lt Gen Olusegun Obasanjo (1976); Alhaji Shehu Shagari (1980)and Gen Muhammad Buhari (1984) respectfully to encourage people to farm and return to their abandoned farms. | An ƙaddamar da waɗannan shirye-shirye guda uku a zamanin tsohon shugaban mulkin soja Lt Gen Olusegun Obasanjo (1976) da zamanin mulkin Alhaji Shehu Shagari (1980) da kuma zamanin Gen Muhammadu Buhari (1984) don zaburar da mutane su koma su yi noma a gonakinsu da suka bari. |
These are the factors that determine the prices of agricultural produce. | Waɗannan sune dalilai dake yanke farashin kayan amfanin gona. |
Cattle, sheep, pigs, poultry and dwarf goats are reared. | Ana kiwon shanu, tumaki, alade, kaji da dodanniya. |
(d) Mention one state where the following animals are mostly reared (i) goats (ii)fish (iii) bull (iv)fowl | (d) Ambaci wata jiha da ake kiwon dabbobi masu zuwa (i) awaki (ii) kifi (iii) sa (iv) tsuntsaye. |
Bush fowl(Gallus spp), Snail (Archachatinamorgunata). | Tsuntsayen daji (Gallus spp), katantanwa (Archachatinamorgunata). |
19. Deforestation increases the following EXCEPT (a) desert encroachment (b) leaching of plant nutrients (c) loss of organic matter (d) moisture retention (e) soil erosion | 19. Sare itatuwa yana kara waɗannan IN BAN DA (a) kwararowar hamada (b) sararewar sinadaren tsirrai (c) rasa sinadaran ƙasa (d) riƙe lema (e)zaizayar ƙasa |
1. (a) Define Agriculture (b) State ten importance of agriculture | 1.(a) Yi bayanin menene noma (b) Zayyano amfanin noma guda goma. |
102. A marketing activity which involves the grouping of produce into various weight and sizes is known as …… A. advertisement B. grading C. packaging D. storage | 102. Kasuwanci wanda ya ƙunshi raba kayan amfanin gona zuwa mabambantan nauyi da girma, shi ake kira___________ A. talla B. darajantawa C. ɗaurewa D. ajiyewa |
6. Soil science : This branch of agriculture deals with the study of soil structure, formation, texture and nutrients. | 6. Ilimin Kimiyyar Ƙasa: Wannan fanni ya ƙunshi karantar ilimin siffar ƙasa da abin da ya samar da ita da kaurin ta da sinadaran ta. |
Cold stores provide large, volume, long –term storage for strategic food stocks in case of national emergency in many countries. | Shagunan sanyi suna ba da manya da girma da dogon lokacin ajiyar don dabarun adana abinci mai muhimmanci saboda buƙatar gaggawa ta ƙasa a ƙasashe da yawa. |
(2) Write out materials that are used in agro allied industries | (2) Rubuta kayan aiki da ake amfani da su a masana'antun harkokin noma |
FARM YARD MANURE:It is a mixture of animal droppings, urine, food remains and beddings or litter. | TAKIN GIDAN GONA: haɗaka ce ta kashi, fitsari,ragowar abinci, shimfiɗar ciyawa, da kuma sharar dabbobi. |
Farm animals have certain basic features that make them belong to a particular group .These characteristics help to differentiate them from other forms of animals and also enable some of the animals to adapt to their natural habitat . | Dabbobin noma suna da wasu siffofi na asali waɗanda ke sa su kasance cikin rukuni na musamman Wadannan sifofin suna taimakawa wajen bambanta su da sauran nau'ikan dabbobi kuma suna ba da damar wasu daga cikin dabbobin su saba da muhallinsu. |
Subject : AGRICULTURAL SCIENCE Term : FIRST TERM Class : JSS 3 / BASIC 9 | Maudu'i : KIMIYYAR GONA, Zango: Na FARKO : JSS 3 / BASIC 9 |
Explain the following: a) Agricultural extension b) Forestry | Yi bayanin waɗannan: a) Fannin Faɗaɗa Ilimin Noma Da Kiwo b) Ilimin Raya Gandun Daji |
Objectives | Zaɓi ka Tiƙa |
PIG: They are most productive of all farm animals . | ALADE: Su ne mafi yawan haihuwa a dabbobin kiwo., |
There is low incidence of pests and diseases | Akwai ƙarancin yaɗuwar ƙwari da cututtuka. |
4..What are aquatic animals ? | 4. Menene ma'anar dabbobin ruwa? |
Pneumonia affects what part of the animal body A. Brain B. Lungs C. Intestine D. Skin | Wacce gaɓa ce cutar Pneumonia take kamawa daga cikin jikin dabbobi A. Ƙwaƙwalwa B. Huhu C. Hanji D. Fata |
Some animals were kept and later gave birth to young ones, also some of the fruits that were thrown away later germinated and bore fruits, | Wasu dabbobin an killace su, daga baya suka riƙa haihuwa, haka nan wasu daga cikin 'ya'yan itatuwan da ake zubarwa, daga baya sun canza zuwa 'ya'yan itatuwa. |
8 Thekind of Agriculture in which farmers produce enough to feed himselfand excess is sold is called ____ | 8. Irin nau'in noman da manomi ke noma amfanin gonar da zai ishe shi har ya saida rara shi ake kira da ____ |
ACTIVITIES AT THE CHANNELS OF DISTRIBUTION OF AGRICULTURAL PRODUCE | Ayyukan Da Ake A Kafofin Rarraba Amfanin Gona |
5. DISEASES: Disease is a situation in plants or animals in which there is a deviation of the plant or animal from normal state of health. | 5. CUTUTTUKA: Cuta wani yanayi ne a cikin tsirrai ko dabbobi inda ake samun karkacewar shuka ko dabba daga yanayin lafiya na yau da kullum. |
It is therefore a profit-oriented venture/enterprise. | Don haka kamfani/kasuwanci ne mai dogaro da riba. |
livestock affected = cattle | Dabbobin da ta ke kamawa: shanu |
3. PERENNIAL CROPS: – These are crops which grow and complete their life cycle in more than two years e. g. banana, orange, cocoa, coconut etc. | 3. Ƴan fiye da shekara biyu: waɗannan sune amfanin gona da suke girma kuma su cika tsarin rayuwarsu a fiye da shekara biyu, misali: ayaba, lemon fata, koko, kwakwa, dss. |
52. In selecting a farmland site, the following factors are put into consideration except ……. | 52. A lokacin zaɓar filin da za a yi noma, ana duba waɗannan abubuwa in ban da_________ |
ROLES OF GOVERNMENT AGENCIES IN AGRICULTURAL PRODUCTION. | RAWAR DA HUKUMOMIN GWAMNATI KE TAKAWA A FANNIN NOMA DA KIWO |
These are diseases caused by viruses. | Wayannan sune cutukan virus ke sanya wa dabba |
2. Agricultural engineering : This is concerned with the study of farm machineries and their uses. | 2. Ilimin Aikin Injiniyan Noma Da Kiwo: Wannan fannin ya shafi karantar injinan aikin noma da amfaninsu. |
The supervision of accounts and bookkeeping of all operations on the farm is carried out by ____ A. Farm treasurer B. bookkeeper C. Farm managers D. Farm supervisor | ____ ne ke sa ido kan asusu da lissafin harkokin kuɗi kan duka ayyukan da ake yi a gona. A. Ma'ajin gona B. Mai lissafin harkokin kuɗi C. Manajojin gona D. Mai sa ido kan gona |
Of all animals living in water, fish is the most plentiful of them. | A cikin dukkan dabbobin da ke rayuwa a cikin ruwa, kifi ya fi komai yawa |
(IX) The bones of fish can be crushed and processed into fertilizers. | (IX) Wajen da ake kiwon kifi na iya samar da nishaɗi da samr da ilimi ga ɗalibai masu koyon fasahar noma da kiwon kifi. |
The replacement of seeds that fail to germinate is called _________ (a) supplying (b) thinning (c) mulching (d) weeding | Musayar irin da ya ƙi hudowa shi ake kira ____________ (a) musanyawa (b) sassabewa (c ) rufewa (d) nomewa |
What are annual crops.? | Menene tsirran shekara-shekara? |
Subject : Agricultural Science, Term : Second Term, Class :Jss 1, Year 7 | Darasi: Kimiyyar Noma, Zangon Karatu: Zango Na Biyu, Aji: Aji 1 na ƙaramar Sakandire, Shekara ta 7 |
Fish is high in demand for health today because of low cholesterol (unsaturated fat ) content. | Kifi wani abu ne da ake matuƙar buɓata saboda ba ya ɗauke da sinadarin kwalastaral mai sanya ƙiba ajikin ɗan adam. |
Forms of Labour available to farmers are: | Nau'o'in aiki ga manoma sune: |
Fish and meat kept in this way can remain in good condition for a long time. | Kifi da naman da aka ajiye ta wannan hanyar na iya kasancewa cikin yanayi mai kyau na dogon lokaci. |
Make a ten list of the example of the following: Mammal, Non-mammals | Kawo misalai guda goma na waɗannan: Dabbobi masu shayarwa, Marasa shayarwa, |
49. Cotton stainer is classified as ……. Insect A. biting and chewing B. piercing and chewing C. piercing and boring D. piercing and sucking | 49. Mai ɓata audugu yana cikin rabe-raben ____________ A ƙwari B. hudawa da taunawa C. hudawa da watsarwa D. hudawa da tsotsa |
Application of manures like compost, green and farm yard manures. | Sanya takin gargajiya, kamar su takin ruɓa, takin ganye, takin kashin dabbobi. |
It gradually reduces the strength and vigour of succeeding generations | A hankali yana rage ƙarfi da kuzarin na tsararrakin masu maye gurbi a gaba |
symptoms = the udder becomes swollen, reddened and painful | Alamomin kamuwa: nono yakan kumbura, yayi ja, kuma yana zafi |
Ideally, the total pore space should be 50% of the soil volume. | Asali, ya kamata jimillar sararin kafofin su ɗauki kaso 50 cikin 100 na yawan ƙasa. |
1. Tractor: For pulling Farm implements and machines such as plough, harrows and planters, For driving other farm machinery. | 1. Tarakta: Don jan kayan aikin gona da injuna irin su garma, harrows da shuka, Don tuƙi sauran injinan gona. |
2.State 3 advantages and 2 disadvantages of mixed farming system. | 2. Kawo fa'idoji 3 da rashin fa'idoji 2 na noman gaurayawa. |
Land is limited in supply (its amount cannot be increased in a geographical area) and thus its availability for agricultural practise is largely dependent on | Gona nada iyaka wajen samu (ba a ƙara yawanta a faɗin wurin da take) saboda haka samunta don yin noma ya dogara ne kacokan akan |
(a) Government should subsidize the price of agricultural inputs | (a) Ya kama gwamnati ta sanya tallafi ga kayan noma. |
1 _________ is an area of land for growing crops and or raising farm animals A. School farm b. Class room C.Dining hall D. sport complex E. Bath room | 1...... wani yanki na ƙasa da ake noma tsirrai da ko kuma kiwon dabbobi. A. Gonar makaranta B. Aji C. Dakin cin abinci D. Wuraren gudanar da wasanni E. Kewayen wanka (banɗaki) |
5. State five problems of agricultural development in Nigeria and suggest two possible solutions to each. | 5. Zayyano matsaloli biyar da suka hana cigaban noma da kuma shawarwari biyu na warware kowacce. |
Water-logging – this also reduces soil fertility and land for farming. | Ambaliyar ruwa – itama tana rage yawan albarkar ƙasa da kuma yawan ƙasar noma. |
They are operated by a man walking behind them and used mainly for light cultivation. | Mutum mai tafiya a bayansu ne ke sarrafa su, kuma ana amfani da su ne don ƙaramar noma. |
A management committee is elected on a one-member one-vote basis to direct the affairs of the cooperative. | Ana zaɓen kwamitin gudanarwar ƙungiyar ta hanyar ƙuri'a daga kowane 'yan ƙungiya |
Labour includes all forms of productive human efforts put into or utilized in production. | Aiki ya ƙunshi dukkan nau'ukan sarrafawa ta hanyar ƙoƙarin da ɗan Adam yayi, ko yayi amfani dashi wurin sarrafawa. |
3 Little labour is required in preserving the food. | 3 Ba a buƙatar aiki mai yawa don adana abinci ta wannan hanya. |
6. Fibre is the raw material for ____ industries (a) drugs (b) food (c) beverages (d) textile | 6. Auduga amfann gona ne don masana'antun____ (a) magunguna (b) abinci (c) abun sha (d) tufafi |
Hilly and sloppy surfaces support erosion and encourage soil formation. | Tudu da gangara suna ƙarfafar zaizayar ƙasa da kuma taimakawa samarda ƙasa. |
Which of these is not a role of science and technology in agriculture? | Wannan ne ba ya cikin rawar da kimiyya da fasaha ke takawa a fannin noma da kiwo. |
98. Which of the following is not a method of fertilizer application? A. row placement B. top dressing C. broadcasting D. branding | 98. Wanne ne a cikin waɗannan ba hanyar zuba taki ba? A. zubawa a layi B. shiryawa a sama C. yaɗawa D. alamtawa |
This includes watering, weeding, applying fertilizers, pruning, weeding etc. | wannan ya kunshi banruwa, noma, zuba taki, aski, da sauransu |
i. Farm record ii Profit and loss account iii Consumption Record iv Inventory v Farm diary. | i. Bayanan da ake ajiyewa a kan gona II. Asusun da ke ɗauke da riba da kuma asara. III. Bayanin adadin yawan abubuwan da ake amfani da su IV. Kayayyakin da ake da su a hannu V. Littafin da ke ɗauke da muhimman bayanai a kan gona. |
It protects the soil against erosion | Yana kare ƙasa daga zaizayewa |
2. State 5 properties of each types of soil mentioned in (i) above | 2. Lissafo siffofi 5 na kowanne nau’in ƙasa da aka ambata a tambaya ta (1) a sama |
Rock constitutes a significant part of the earth’s crust. | Dutse yana tattare wani sashi mai mahimmanci na duniya. |
These duties includes supervision of the work on the farm, arrangement work roasters, directing workers on day-to-day activities,ensuring staff welfare, organizing training of man-power in the farm, etc. | Waɗannan ayyuka sun haɗa da sa ido kan aikin gona, tsara waɗanda za su yi aiki da lokacin da za su yi aiki, bada umarni ga ma'aikata kan gudanar da ayyukan kullum, kula da jin daɗin ma'aikata, tsara horar da ma'aikata a gona, da dai sauransu. |
35. The knowledge of packaging materials is essential because each product to be packsged has its own (a) direction (b) shape (c) properties (d) size | 35. Ilimin sanin yadda ake shirya kaya a mazubi yana da muhimmanci saboda duk kayan da za a zuba a mazubin yana da nasa (a) alƙibla (b) siffa (c) abubuwan da ya ƙunsa (d) girma |
Rabbits: Cities where poultry are successfully reared. | Zomaye: Biranen da akayi kiwon kaji cikin nasara. |
Producers: These are the farmers that are responsible for the direct production of crops and livestock. | Masu samarwa (manoma): Waɗannan sune manoma wanda suke samar da amfanin gona da dabbobin kiwo. |
Objective Test: | Gwajin Canki-canki: |
It is a source of medicinal herbs, It is a source of fibre and ropes | Daji yana samar da magungunan gargajiya. Kuma yana samar da abin ci da igiyoyi |
Periodic Maintenance of Farm Machinery | Bayar da Kula ga Injinan Aikin Gona Lokaci-lokaci |
Fowl is the most popular of all and this makes the discussion on poultry to be centred on domestic fowl .Domestic fowls are grouped into two :Local fowl and Exotic fowl. | Kaji su ne mafiya shahara kuma wannan yasa tattaunawa akan kiwon tsuntsu ya ta'allaka ne akan kajin gida. An kasa kajin kiwo zuwa kashi biyu; na gida da na alfarma. |
Name the 5 major feed nutrients | Kawo sunaye biyar (5) na manyan sinadaren abinci masu amfani ga jikin dabba |
A bank account will be opened for the society with about three signatories to the account. | Za a buɗe asusun banki na ƙungiyar ɗauke da masu sa hannu aƙalla uku domin fitar da kuɗi.. |
State any 3 functions each of the stem and the root. | Kawo ayyuka 3 na gangar jikin shuka da jijiya. |
Sales of commodities in a local market. | Siyar da kayan siyarwa a ƙananan kasuwanni |
5. Presence of sulphur in the soil. | 5. Wanzuwar sinadarin sulphur a cikin ƙasa. |
This makes it difficult for farmers to transport their products from villages to cities and forces them to sell at local markets at relatively low prices. | Wannan ya sanya manoma ke shan wahala wajen safarar kayan da suka noma daga ƙauyuka zuwa cikin birane, hakan na
tilasta musu sayarwa a kasuwannin cikin gida, kusan a farashi mai rahusa. |
The flowers produce the fruits and seeds | Furen suna samar da 'ya'yan itatuwa da iri |
The following are agricultural practices in West Africa EXCEPT (a)fishery (b)poultry (c)crop cultivation (d)hunting | Waɗannan abubuwa hanyoyi ne na noma a Yammacin Afrika amma banda abu daya shine... (a) kiwon kifi (b) kiwon tsuntsayen gida (c) shuka (d) farauta |
9. Agriculture provides all the following EXCEPT .......A. Food B. Shelter C. Poverty D. Clothing | 9. Noma da kiwo na samar da dukan waɗannan abubuwa, BANDA A. Abinci B. Mahalli C. Talauci D. Tufafi |
It helps in cloud formation | Yana taimakawa wajen haɗuwar gajimare. |
Permeability and Water-Holding Capacity: | Ƙarfin iya Karɓa da kuma Riƙe ruwa: |
The purpose of this is to ensure products quantity and stable price. | Manufar yin wannan aiki ita ce tabbatar da samun amfanin gona da yawa da kuma tsayayyen farashi. |
They are the earliest domesticated and the most widely distributed animals with high concentration in Africa and India .Goat have ability to withstand harsh weather conditions. | Su ne farkon dabbobin gida kuma mafi yawan dabbobin da aka rarraba tare da mafi yawa a Afirka da Indiya. Akuya na da ikon jure yanayi mai tsanani., |
iv) Environmental degradation. | iv) ƙasƙantaccen muhalli |
The temperature is usually maintained between 37.5°C and 39.5°C Setter: | Yawanci ana daidaita zafin ne tsakanin 37.5°C da 39.5°C. Setter: |
End of preview. Expand in Data Studio
README.md exists but content is empty.
- Downloads last month
- 71